1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yabawa Musulman kasar

May 12, 2021

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yiwa daukacin al'ummar Musulman da ke zaune a Jamus fatan gudanar da bikin sallah karama bisa aminci.

Berlin Konzerthaus am Gendarmenmarkt | Rede Steinmeier | Gedenkfeier Covid-Opfer
Hoto: Michael Sohn/AFP/Getty Images

Steinmeier ya nuna juyayi kan yadda za su gabatar da bikin cikin tsauraran matakan hana yaduwar cutar corona a karo na biyu. Sai dai ya ce da alamun haske a allurar rigakafin annobar da ake sa ran za ta kawo karshen wahalhalun da aka fuskanta.

A sakonsa ta faifan bidiyo, Steinmeier ya kuma mika godiyarsa ga musulman Jamus bisa yadda suka jajirce wajen bin dokokin annobar na takaita haduwa tun daga watan Maris din bara. A nan Jamus ma a ranar Alhamis take ranar karamar sallah. Alkalumma na nuna cewa kimanin musulmai miliyan 4 ne ke zaune a Jamus.