1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta yi kira da a aiwatar da sauye sauyen siyasa a Aljeriya

January 7, 2012

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya na gudanar da ziyarar aiki a Algers a inda ya yi kira ga hukumomin wannan kasa ta Alejriya da su aiwatar da sauye sauye.

Aussenminister Guido Westerwelle (FDP, l.) und der algerische Aussenminister Mourad Medelci geben am Samstag (07.01.12) in Algier, der Hauptstadt von Algerien, eine Pressekonferenz. Ein Jahr nach Beginn der politischen Umbrueche in Nordafrika ist Westerwelle am Samstag in die Region geflogen. (zu dapd-Text) Foto: Thomas Trutschel/Pool/dapd
Ministan harkokin wajen Jamus Westerwelle a hannun hagu da na Algeria Mourad Medelci a dama.Hoto: dapd

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya isa ƙasar Aljeriya da ke zama zangon farko na rangandin kwanaki huɗu da zai gudanar a wasu ƙasashe na arewacin Afirka. A lokacin da ya ke bayani bayan da ya gana da takwaran aikansa na Aljeriya Mourad Medelci, Westerwelle ya yi kira ga hukumomin Algers da su aiwatar da sauye sauyen da suka dace. kana ministan na Jamus ya bayyana farin cikinsa game da amincewa da Aljeriya ta yi da buɗe wa 'yan kallo na ƙetare ƙofofita, domin su je su sa ido a zaɓɓukan gama gari da za su gudanar a watan Afirilu mai zuwa.

Westerwelle zai gana nan gaba da firaministan Aljeriya Ahmed Ouyahia, da kuma ministan masana'antu da ma dai 'yan kasuwan ƙasar, kafin ya zarce zuwa ƙasashen Libya da kuma Tunisiya. Ministan harkokin wajen na Jamus na wannan ziyarar aikin ne, da nufin kyautata dangantakar cinikayya tsakanin ƙasarsa da kuma ƙasashen na arewacin Afirka, tare da nuna musu goyon baya ga yunƙurin da suke yi na tabbatar da wanzuwar demokaraɗiya a cikinsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdullahi Tanko Bala