Jamus ta yi na'am da shawarar Macron kan EU
March 5, 2019Talla
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran yin gyaran fuska ga gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai, a kan matsalolin da ka iya tasowa sanadiyar masu nuna tsantsar kishin kasa a Turai. Kiran nasa na zuwa ne kimanin watanni uku a gudanar da zaben 'yan majalisun dokokin Tarayyar Turai. Ya yi nuni da cewa, ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai a ranar 29 ga watan Maris, na nuni da irin kalubalen da Tarayyar Turai ke fuskanta.
Gwamnatin Jamus, ta bakin mataimakin shugabar gwamnatin Jamus kuma ministan kudi Olaf Scholz, yace gwamnatin Jamus na goyon bayan shawarar ta Macron.