1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta samu bunkasar tattalin arziki

February 15, 2024

Sabin alkalluman tattalin arziki sun nunar da cewa Jamus ta karbe matsayi na uku daga hannun Japan na kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya a shekarar 2023.

Deutschland | Bundestag Generaldebatte Haushalt | Olaf Scholz
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Alkaluman da aka fitar a ranar Alhamis 15.02.2024 sun nunar da cewa jimilar karfin tattalin arzikin Japan a shekarar 2023 ya tashi a tiriliyan 4,2 na dalar Amurka idan aka kwatanta da na Jamus da ya kai tiriliyan 4,5. 

Karin bayani: Scholz: Jamus za ta fita daga matsin tattali da take ciki

Kafafan yada labaran Japan sun alakanta wannan koma baya da faduwar darajar kudin kasar wato Yen akan dalar Amurka da kusan kashi 18% tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023. Baya ga haka Japan na fuskantar koma bayan fusahar kere-kere da kuma raguwar karfin hada-hadar kasuwanci da kasashen duniya.

To sai dai ita ma Jamus da ta yi nasararar darewa wannan matsayi na fama da matsaloli na raguwar fitar da hajoji kasashen ketare da kuma tsadar makamashi da ke raunana tafiyar masana'antunta na cikin gida.

Ana sa ran nan da 'yan shekaru masu zuwa kasar Indiya da a halin yanzu ke kan gaba wajen yawan al'umma a duniya ta zarta kasashebn na Jamus da Japan da ke a matsayin na uku da na hudu a fannin karfin tattalin arziki.