1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai na zargin Rasha da satar bayanai

Zulaiha Abubakar
October 5, 2018

Gwamnatin Jamus ta sanar da dora alhakin wani mummunan kutsen bayanan sirrinta a kafar Internet da ya faru a shekara ta 2015 kan kasar Rasha.

Angela Merkel und Wladimir Putin Kombobild
Hoto: picture-alliance/dpa/Gambarini/Druzhinin

Sanarwar ta kara da cewa Tarayyar Jamus na da tabbas kan wannan zargi biyo bayan binciken da ta gudanar kan wata manhaja mai lakanin  APT 28  a Internet mallakar hukumar leken asirin Rasha. Sanarwar ta ja hankalin gwamnatin Rasha kan ta mutunta dangantakar da ke tsakaninta da kasashen kawance. Wannan zargi dai na zuwa ne bayan da kasashen Amirka da Birtaniya da kuma Netherland suke ci gaba da zargin Rashan da leken asirin al'amuran gudanarwar kasashensu. Har ya zuwa yanzu dai babu wani martani daga bangaren Rashan.