1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: takaddama tsakanin CDU da CSU

April 19, 2021

Kawancen jam'iyun CDU da CSU a tarayyar Jamus sun gaza cimma matsaya dangane da wanda zai wakilci kawancen jam'iyyun a babban zaben kasar da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa.

Kombobild Armin Laschet und Markus Söder

An dai sanya wa'adin jiya Lahadi domin kawo karshen takaddamar kan wanda zai gaji shugabar gwamnatin Angela Merkel nan da watan Satumbar, tsakanin Armin Laschet na jam'iyar CDU da Markus Soeder na jam'iyar CSU.

Yan takarar da magoya bayansu sun fara wannan tattaunawar ce tun a makon da ya gabata, inda aka kyautata zaton kawo karshenta a jiya Lahadi, sai dai abin ya faskara, bayan kwashe sa'oi uku ana murza gashin baki a ginin majalisar dokokin kasar ta  Bundestag.