1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Tallafawa Ukraine nauyi ne a kan dukkan kawayenta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 2, 2025

Kasashe 30 kawayen Ukraine za su yi taro a birnin Paris don tattauna hanyoyin bai wa Ukraine kariya daga mamayar Rasha.

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, ya ce ba wai tarayyar Turai ce kadai ke da alhakin daukar gabaren aikewa da dakarun tsaro don agazawa kasar Ukraine ba.

Mr Merz na fadin hakan ne a matsayin martani ga jawaban da shugabar hukumar gudanarwar tarayyar Turai EU Ursula von der Leyen ta yi kan wannan batu, yana mai jaddada cewa samar da dakarun ya rataya a wuyan kawayen Ukraine baki-daya.

Wannan na zuwa kwana guda bayan da aka jiyo makamantan kalaman na Mr Merz daga bakin ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, a ranar Litinin, biyo bayan rahoton da jaridar Financial Times ta wallafa, wanda ta rawaito Ursula von der Leyen na zayyana tsare-tsaren da za a yi amfani da su wajen tura sojojin agaji Ukraine.

A ranar Alhamis kasashe 30 da ke zama kawayen Ukraine, za su yi taro a birnin Paris na Faransa, don tattauna hanyoyin bi na bai wa Ukraine kariya daga mamayar da Rasha ke mata na sama da shekaru uku.

karin bayani:Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus ya kai ziyara Ukraine

A gefe guda kuma kasashen Turai da ke kawance da Ukraine sun ce tallafin Amurka suke dako, kan batun bai wa Ukraine tabbacin kariyar tsaro daga sake fuskantar wata mamaya, da zarar an kai gabar cimma yarjejeniyar dakatar da yakin da kasashen biyu ke gwabzawa.

Wata sanarwa da fadar shugaban Faransa Emmanuel Macron ta fitar a wannan Talata, ta ce wannan ne babban muradin da suka sanya a gaba, na ganin an samar da masalaha da daidaito a kan wannan yaki.

Hakan na zuwa ne gabanin ganawar shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine da aminansa a Faransa ranar Alhamis.