1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Tsokacin AfD kan 'yan gudun hijira

Abdullahi Tanko Bala SB
August 17, 2017

Babban dan takara na jam'iyyar AfD a nan Jamus Alexander Gauland ya bukaci Jamus da kasashen Turai su rufe iyakokinsu domin hana wadanda ya kira mutanen da ba su da izinin shiga cikin kasashen.

Deutschland wählt DW Interview mit Alexander Gauland AfD
Dan takarar jam'iyyar AfD ta kasar Jamus Alexander GaulandHoto: DW/R. Oberhammer

Shi dai Alexander Gauland shi ne babban dan takara na jam'iyyar AfD a babban zaben gama gari da za'a gudanar a nan Jamus a watan Satumba mai zuwa. Kuma a hirar da ya yi da tashar DW, dan siyasar mai shekaru 76 a duniya ya ce kuskure ne barin shigowar wadanda ba su da takardu cikin kasar kuma ko kadan bai kamata Jamus ta sake mutanen da basu da cikakkun takardu su shigo cikin kasar ba:

"Ya kamata a rufe kan iyakoki kada a bar wanda ba shi da takardar izinin shigowa tsallaka iyakokin mu ba." 

A ra'ayin dan takarar na jam'iyyar AfD Alexander Gauland, mutanen da ke tserewa a yankunan da ake yaki kamar Siriya suna da damar samun mafaka amma 'yan kalilan kawai kamar yadda yake kunshe a yarjejeniyar Geneva:

Dakatar da kwararar wadanda basu da takardun Jamus

'Yan jarida na hira da Alexander Gauland dan takarar Jam'iyyar AFD a JamusHoto: DW/R. Oberhammer

"Wadannan mutane kwata-kwata bai kamata a bari su shigo kasar nan ba. Ya kamata su kasance ne a cibiyoyi na masu neman mafakar siyasa a wajen Jamus, ko ma a wajen nahiyar Turai inda daga nan ne ya kamata su mika bukatarsu ta neman mafaka idan har ma sun cancanta a basu."

A cewar Alexander Gauland Yawancin mutane suna gudun hijira ne saboda dalilai na tattalin arziki. Sai dai ko da yake suna da 'yancin neman kyautatuwar rayuwa, ya ce haka ita ma kasa tana da 'yancin hana su mafaka.

"Ya kamata mu yi la'akari da namu muradun, amma karbar dubban 'yan gudun hijira, ba abu ne da ya dace da bukatun Jamus ba, kuma Jamus ba tuma kasa bace da kowa daga kasashen duniya zai shigo mata. Yawancin 'yan gudun hijirar don radin kan su suke zuwa daga kudancin Afirka su bi ta Libya, saboda haka duk wanda ya zo ta Libya don radin kansa, ya kamata a mayar da shi inda ya fito."

Jam'iyyar AfD na adawa da shigar Marassa takardu Jamus

'Yan gudun hijiran Siriya da Afghanistan bisa hanyar teku zuwa TuraiHoto: Getty Images/A. Koerner

Batun yan gudun hijira dai ya zama wani batu na yakin neman zabe. Jam'iyyar ta AfD, farin jininta ya karu a lokacin da ake tsananin matsalar kwararar 'yan gudun hijira a 2015. Manufar Jamus kan 'yan gudun hijira na daya daga cikin muhimman batutuwan da jam'iyyar ta sanya a gaba a yakin neman zabe. Jami'yyar ta sami kujerun majalisun dokoki a jihohi 13 daga cikin jihohi 16 na Tarayyar Jamus, kuma akwai yiwuwar a karon farko za ta sami shiga majalisar tarayya a zaben da za a yi a ranar 24 ga watan Satumba. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna za ta iya samun kashi takwas cikin dari na kuri'un. Kashi biyar ne dai cikin dari doka ta iyakance adadi mafi kankanta da jam'iyya za ta samu a zabe kafin ta sami shiga majalisar dokoki.