Jamus: Turkawa ba sa fiskantar barazana
September 11, 2017Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a ranar Lahadi cewa babu wani dalili da zai sanya al'ummar kasar Turkiyya da ke son zuwa Jamus su sanya fargaba a zukatansu .
"A wajenmu babu wani dan Turkiyya da aka haramta masa ya shiga Jamus, babu wani dan jarida da za a tsare kan batu na fadin albarkacin baki ba dalili na sanya masa linzami."
Merkel na mayar da martani ne ga kasar ta Turkiyya wacce ke zargin cewa 'yan kasarta da ke son zuwa Jamus za su iya fiskantar tsangwama ko nuna wariya ko kai musu hari na ta'addanci. Ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar ta Turkiyya ce dai ta ba da wannan gargadi a ranar Asabar, inda suka yi gargadi ga matafiya zuwa kasar ta Jamus da su yi takatsantsan a lokacin ziyararsu a Jamus za su iya fiskantar barazana a lokacin yakin neman zabe, don za su ga masu kyamar Turkawa saboda zargi na daukar aiyukan ta'addanci.