Jamus: 'Yan sanda sun kai sumame
August 10, 2016Jami'an 'yan sanda a Jamus sun kai sumame zuwa wurin aiki da gidajen wasu mutane uku, da ake zargi da shirin horar da mutane domin shiga Kungiyar IS, a cewar ofishin babban mai shigar da kara na gwamnati.Sai dai ba'a kama kowa ba.
Ana zargin daya daga cikinsu da tallafa wa kungiyar 'yan ta'addan na IS a bangaren kudi da sufuri. Sumamen na yau Laraba ya gudana ne a jihohin North Rhine-Westphalia da Lower Saxony.
Frauke Köhler ita ce kakakin babban ofishin shigar da kara na tarayya a birnin Kalsruhe:
" Ta ce binciken da muka gudanar ya nunar da cewar, mutanen uku 'yan Salafiyya ne. Sun bayyana cewar sun koyar da darussa na addini da Salafiyya, salon na yin jihadi ga mutanen da ke shirin barin Jamus, domin su samu damar shiga kungiyar 'yan ta'adda ta IS".Kafofin yada labaru na Jamus dai sun shaidar da cewar binciken ya gudana ne a garuruwan Duisburg da Dortmund da Düsseldorf da kuma Hildesheim.Jamus din dai ta dauki tsauraran matakan tsaro tun bayan har- hare biyu da suka auku a watan Juli, wadanda suka kashe masu kai harin su ka dai.