1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da yakar corona ya watse

Zainab Mohammed Abubakar
August 29, 2020

An tarwatsa gangamin adawa da tsananta matakan yaki da annobar corona a Jamus, wanda dubban mutane suka halarta a birnin Berlin, biyo bayan keta ka'idojin kariya na cutar.

Deutschland Berlin Protest gegen Corona-Maßnahmen
Hoto: Reuters/C. Mang

 

Sanarwar ta bayyana takaicinta na dakatar da gangamin bayan tuntubar jagoran shiryashi, kasancewar 'yan sandan basu da wani zabi.

Rundunar ta ce mutane sun ki sanya tazara a tsakanin junansu, kana da yawa basu sanya takunkumin kariya ba saboda kaucewa kamuwa ko kuma yaduwar COVID-19. 

Bayan dogon lokaci na mahawara da masu shirya zanga-zangar da ta samu halartar mutane dubu 18, 'yan sanda suka sanar da matakin wargaza ta. Jami'an 'yan sanda dubu uku nedai aka girke a wurin gangamin.