1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin sake gina gidaje bayan ambaliya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2021

Kwanaki bayan ibtila'in ambaliyar da ya kassara hanyoyi da gidaje, baya ga salwantar rayukan jama'a a Jamus, an ware makudan kudaden tallafa wa jihohin da matsalar ta yi kamari.

Deutschland Unwetter l Aufräumarbeiten in Bad Neuenahr
Hoto: Thomas Frey/dpa/picture alliance

Mako daya bayan mummunan ibtila'in ambaliyar da ya shafi yammaci da arewacin Jamus, gwamnatin kasar ta ware euro miliyan 200 daga baitul malinta dan tallafawa wadanda matsalar ambaliyar ta shafa.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da su kuma hukumomin yankunan da matsalar ta fi kamari, za su samar da tallafin gaggawa na euro miliyan 400 ga jama'a, a matsayin agajin sake inganta gidaje da hanyoyin da suka ruguje a jihohin biyu, daya ta Arewa da ta yammacin Jamus.