Jamus: Gwajin allurar rigakafin Corona
April 22, 2020Talla
Wannan shi ne gwaji na hudu a fadin duniya na samfurin maganin kariya game da cutar Corona. A matakin farko na gwajin, za a gudanar da shi ne a kan mutane masu koshin lafiya kimanin 200 wadanda shekarunsu ya kama daga 18 zuwa 55 kafin daga bisani gwajin ya kai ga mutane da ke da hadarin kamuwa da cutar.
Kamfanin na Biontech ya sanar da cewar nan bada jimawa ba za a fara wannan gwajin.
Kawo yanzu dai kasashe na ta fadi tashin ganin sun sami rigakafin wannan annobar. Kasar Amirka ma na gab da fara irin wannan gwajin a kan mutane.