1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Za a kawo karshen dokokin Corona

June 1, 2021

Gwamnatin Jamus ta bayar da sanarwar janye dokokin Corona kwata-kwata a kasar, daga nan zuwa karshen wannan watan na Yuni da muke ciki tare da kawo karshen zagaye na uku na annobar.

Deutschland Angela Merkel
Hoto: Markus Schreiber/AFP

Sai dai mahukuntan sun ce, kasar ka iya komawa cikin kullen ma damar aka fuskanci wobuwar annobar, abin da ba a fata in ji shugabar gwamnatin kasar uwar gida Angela Merkel.

Haka zalika kuma shugabar gwamnatin ta godewa al'umar kasar bisa biyayyar da suka yi wa gwamnati a tsawon lokacin da aka share a cikin matsin dokokin yaki da COVID-19.