1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta aike wa Ukraine da tankokin yaki

Binta Aliyu Zurmi
February 15, 2023

Mahukunta a Jamus sun sanar a wannan Larabar za su aike wa Ukraine tankokin yaki masu yawa samfurin Leopard 2, domin ci gaba da kare kanta a yakin da suke yi da Rasha.

Deutschland Verteidigungsminister Pistorius auf einem Leopard 2
Hoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images

Wannan sanarwar ta fadar gwamnatin a Berlin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke fadi tashin ganin ta kara aike wa Ukraine din manyan makamai amma banda jiragen yaki.

Ministan tsaron Jamus Boris Pistorious ya ce alkawarin da suka dauka a watan da ya gabata na aike wa da batallion guda na tankokin yakin ba zai yiwu ba a wannan lokacin amma nan da karshen watan gobe za su aike da rabin abin da suka yi alkawari, kazalika ana sa ran samun karin wasu tankokin daga kawayen Ukraine nan bada jimawa ba.

kasashen Jamus da Poland da Ukraine da wasu mambobin NATO sun gana bayan taron Brussels don ganin sun samar wa Kyiv da isasun tankunan yakin.