Jamus za ta ba da tallafi ga Ecowas
January 16, 2013Talla
Jiragen saman dai zasu tallafa ga yaƙin da sojojin ƙasar faransa da na nahiyar Afirka ke yi da yan tawayen Mali.A wani taron manema labarai da ministan tsaro na ƙasar ta Jamus thomas de Maiziere ya yi tare da ministan harkokin waje waɗanda sun ce jiragen zasu shiga hannu ƙungiyar ta ECOWAS nan bada daɗewa ba.
Yanzu haka manyan kwamandojin soja na ƙungiyar ta Ecowas na can na gudanar da taro a ƙasar Cote d'Ivoire domin tattauna maganar ta aikewa da dakarun yankin na yammacin Afirka zuwa Mali, a sa'ilin da faɗa ya rincaɓe tsakanin sojin Faransa da ke damafama dakarun gwamnatin da na yan tawayen a yankin arewacin Mali.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman