1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamus za ta bai wa Afirka rigakafin cutar Kyandar Biri

August 27, 2024

Gwmanatin kasar Jamus za ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar Kyandar Biri guda dubu 100 domin mika su ga inda aka samu bullar cutar a nahiyar Afirka.

Alluran Rigakafin Kyandar Biri
Alluran Rigakafin Kyandar BiriHoto: abaca/picture alliance

Fadar gwamnati da ke birnin Berlin, ta ce kasar ta Jamus na kokarin daukar matakai ne cikin hanzari ne domin bai wa musamman Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da cutar ke ta'adi a cikinta tallafin na rigakafin cutar Kyandar Biri.

Haka zalika, mai magana da yawun gwamnatin Jamus ya sanar da cewa gwamnatin za ta bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO kudade domin taimaka wa aikin yaki da cutar ta Kyandar Biri.

A farkon wannan watan ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cutar a matsayin matsalar lafiya da ke bukatar mataki na gaggawa a duniya a yanzu.

Haka nan ma an samu wasu da suka kamu da cutara kasashen yankin Asiya da ma nahiyar Turai.