1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta bai wa Ukraine tankokin yaki

Zainab Mohammed Abubakar
January 25, 2023

Gwamnatin Jamus ta amince za ta aika wa kasar Ukraine tankunan yaki samfurin Leopard 2, ta kuma amince wa sauran kasashe abokan kawance da ke muradin yin hakan fitar da wadannan tankunan yaki.

Deutschland Bundeskanzler Scholz spricht vor dem Bundestag
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Kakakin gwamnatin Jamus Steffen Hebestreit ya ce Berlin na da niyyar aike wa da manyan tankunan yaki guda 14 samfurin Leopard 2A6 daga ma'ajiyarta ta Bundeswehr zuwa Ukraine inda ya kara da cewar kasar za ta kuma amince wa kasashen Turai da ke da niyyar aike wa Ukraine samfurin tankunan yakin kirar Jamus.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sanar da matakin da ya dauka ga majalisar ministocin kasar, bayan da ya fuskanci matsin lamba daga Jam'iyyun kawancen jam'iyyu gwamnatin. A cikin wata sanarwa Scholz ya ce "wannan shawarar ta biyo bayan matakanmu na tallafa wa Ukraine iyakar iyawarmu. Muna yin aiki ne ta hanyar hadin kai a matakin kasa da kasa".

Eric-André Martin kwararre a fannin tsaro, ya ce matakin tamkar yadda ya kasance a baya ne.

Tankin yaki kirar Jamus samfurin Leopard 2 A7VHoto: Moritz Frankenberg/dpa/picture-alliance

"Wadannan manyan tankunan yaki ne kuma wannan ya yi daidai da wani lokaci a baya da kayan yakin tsohuwar tarayyar Soviet suka kai iyaka. A yanzu  an fuskanci koma baya kan makaman da sojojin Ukraine suke amfani da su."

Sanarwar ta kara da cewar, wajibi ne a gaggauta fara horar da jami'an sojin Ukraine a nan Jamuus kan yadda za su yi amfani da wadannan manyan tankunan yaki. Bugu da kari tallafin na Jamus zai hada da sufuri da makamai da kuma kulawa da waddanan kayan yaki.

Tuni dai ake jiran sanarwar bayar da wadannan manyan tankunan yaki daga Berlin zuwa Kiev. Kuma tuni gwamnatin ta Jamus ta karfafa wa sauran kasashe kawayenta gwiwa da su fara bayar da horo ga sojojin Ukraine kan yadda za su yi aiki da tankunan. Kwararre kan harkokin tsaro Eric-André Martin ya yi tsokaci kan wannan matakin na Jamus.

Tankin yaki kirar Jamus samfurin Leopard 2 A7VHoto: Michael Kappeler/dpa/picture-alliance

"Jamus ta ci gaba jan kafa wajen bai wa Ukraine makaman kariya. Ta ki daukar bangare a cikin wannan rikici. Sannan ba al'adar Jamus ba ce ta samar da makamai ga kasar da ake yaki, wanda hakan tilasta mata sauyin alkibla game da wannan al'ada".

A cikin 'yan makonnin da suka gabata, kasashen yammacin duniya sun yi alkawarin samar da karin na'urorin soji da za su taimaka wa Ukraine kan mamayar da Rasha ke yi. Poland ta sha yi wa Jamus matsin lamba kan ta tura tankunan yaki samfurin Leorpard zuwa Ukraine, amma taron da Amurka ta jagoranta a Jamus a makon da ya gabata ya kasa cimma matsaya.

Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya yi gargadin isar da tankunan yana mai cewa ba zai haifar da wani abu mai kyau ga alakar da ke tsakanin Berlin da Moscow ba, kuma zai bar mummunan tabo. Sai dai Faransa ta yi maraba da shawarar da Jamus ta yanke na aike wa da Ukraine da wadannan tankunan yaki.

Gwamnatin Faransa dai na duba yiwuwar aike wa da tankonkinta na yaki samfurin Leclerc mai dauke da bindiga mai tsawon millimita 120 zuwa kasar ta Ukraine.