Jamus: Kokarin bunkasa arewacin Nijar
October 11, 2016Merkel ta ce a shekara daga mai zuwa Jamus za ta zuba miliyan 10 na Euro kan abun da ya shafi samar da kayayakin aikin sojoji, sannan kuma ta ce Jamus na taka rawa a cikin wannan tsari da aka yi wa suna EUCAP mai bada dama wajen horas da jami'an tsaro na 'yan sanda a yakin da ake da 'yan jihadi, sannan kuma ta ce Jamus ta yi alkawarin zuba wasu kudaden Euro miliyan 17 domin bunkasa yankin jihar Agadez a wani mataki na shayo kan matsalar kwararar bakin haure, da kuma munnan safara da ake fuskanta.
Shugaban kasar ta Nijar dai Issoufou Mahamadou ya yaba matakin na Jamus na kafa wata cibiya soja a Nijar domin kula da kayayakin aikin na sojojin da ke ayyukan samar da zaman lafiya a yankin kasar Mali, sannan kuma ya yaba kasancewa sojojin Jamus cikin rundunar MINISMA a yakin da ake da 'yan jihadi kasar ta Mali.