Burkina Faso ta bukaci tallafin Jamus
February 22, 2019A hira da tashar DW, Shugaba Marc Christian Kabore na Burkina Faso ya yaba da tallafin da kasar Jamus ke bai wa kungiyar G5 Sahel wajen tabbatar da tsaro a kasashen yankin sahel, inda ya ce kawo karshen ta'addanci na iya yiwuwa a kasashen biyar idan har kasar Jamus ta dore da bayar da gudumawa ta horar da sojoji da tallafin kayan yaki.
Shugaba Kabore ya kuma bayyana ya gamsuwa da irin matsayar da kasashen biyu suka cimma a yayin ziyarar kan batun mangance tabarbarewar tsaro da ke addabar yankin Sahel.
Shugaba kasar Burkina Faso ya zargi tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da yanzu hakan ke hijira a makwabciyar kasar Côte d'Ivoire tushen tashe-tashen hankulan da ke addabar kasar Burkina Faso.
Shugaban na zargin ne a daidai lokacin da tarbarbarewar tsaro ke ci gaba da zama kalubale ga kasar musamman ma yankunan da ke makwabtaka da Mali.