Alkawalin cika sharadin da NATO ta kafa Jamus na kan hanya
August 1, 2019Talla
Da ta ke magana karon farko a gaban manema labarai bayan ganawarta da babban sakataren zartawar kungiyar NATO a kasar Bejiyam. Annegret Kramp-Karrenbauer ministar tsaron ta Jamus ta ce Jamus na daga cikin abukanin huldar kut da kut na kungiyar tsaro ta NATO kana kuma za ta kara jadadda hakan a gaba.
Ya zuwa yanzu dai kasashe mambobin kungiyar NATO da suka cika wannan sharadi na sanya kaso biyu cikin dari na kasafin tattalin arzikinsu ba su wuce shida ba kawai, a yayin da kasashen kamar Faransa da Jamus da ke a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai suka kasa cimma wannan matsayi, batun da kuma shugaba Donald Trump na Amirka ya sha suka yana mai bayyana cewa kasa yin haka da Jamus ta yi kasawa ce.