1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kudirin rufe tashoshin samar da makamashi

April 11, 2023

Jamus ta kudiri aniyar rufe tashoshin samar da makamashi masu amfani da Nukiliya guda uku da suka rage mata a karkashin wani shiri da zai dauki shekaru goma sha biyar.

Deutschland Atomkraft l Kernkraftwerk Emsland in Lingen
Hoto: Ina Fassbender/AFP

Shirin da za a kaddamar daga wannan Asabar mai zuwa za a kwashe shekaru kusan 15 ana tafiyar da shi a mataki-mataki har a kai ga katse dukannin layukan sadarwa da hanyoyin raba lantarki na tashoshin.

Jamus ta kudiri wannan anniya ce a wani wataki na bada gudunmawa a kokowar da ake da dumamar yanayi da ke addabar Duniya har ma ke haifar da iftila'i da fari a wasu kasashe musanma ma na nahiyar Afirka.  

To sai dai matakin da Jamus ta dauka na zuwa ne a daidai lokacin da wasu manyan kasashen irin su Amurka da Faransa da kuma Burtaniya ke kara karkata izuwa wannan hanya ta samar da makamashi wacce suke gani ta fi cancanta wajen rage dumamar yanayi. Hasali ma Amurka dake sahun farko a jerin kasashe masu cibiyoyin Nukiliya na shirin kara gina wasu cibiyo biyu a kan guda 92 din da ta ke da su a halin yanzu, yayin da Faransa kuwa mai cibiyoyi 56 ke shirin kara gina wasu 14 kafin shekarar 2035 zuwa 2037 sai kuma Burtaniya ita ma da ta yi fice a wannan fanni za ta gina karin wasu tashoshin nukila guda takwas kafin shekarar 2050 bayan dama ta mallaki guda tara.

Jamus dai ta fitar da jaddawali kan wannan shiri nata na ganin cewa nan da shekaru 15 masu zuwa ta kakkabe duk tashoshin Nukiliya da kasar ta share shekaru 60 tana amfani da su.