Jamus za ta dauki matakai kan tashin farashin makamashi
March 20, 2026
Gwamnatin Jamus na shirin amincewa da wata doka domin dakile tashin gwauron zabi da farashin mai ke yi.
Mahukunta a Berlin sun ce ana nazarin kakaba haraji kan kamfanonin mai da ke cin riba fiye da kima, amma sun jaddada cewa lokaci bai yi na daukar tsauraran matakai ba.
Farashin man fetur dai a Jamus ya fara tashin gwauron zabi tun kafin barkewar yakin Iran a karshen watan Fabrairu.
A yanzu farashin dizal ya karu da santi 42 a kowace lita, yayin da man fetur nau'in E10 ya karu da kusan santi 27.
A ranar Laraba, matsakaicin farashi a fadin Jamus din ya kai euro 2.044 kan kowace lita ta E10, yayin da litar man dizal ya kai euro 2.17.
Farashin mai ya sake tashi a jiya Alhamis bayan da Qatar ta sanar da lalacewar wata babbar cibiyar sarrafa iskar gas dinta sakamakon hare-haren Iran.
Gwamnatin Jamus ta kuma bullo da wani tsari na farashin mai, inda ta umurci gidajen mai su rika kara farashi sau daya kacal a rana, amma kuma su rika rage farashi a kowane lokaci.