1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta karfafa matakan kare bayanai

Mohammad Nasiru Awal MAB
January 7, 2019

Ma'aikatar cikin gidan Jamus ta sanar da daukar karin matakan kare bayanai ta intanet bayan an fuskanci satar bayanai daga masu kutse ta intanet.

Illustration - Computer - Cyberkriminalität
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Berg

Bayan sace daruruwan bayanai ta intanet, ma'aikatar cikin gidan Jamus ta sanar da inganta matakan kariya daga masu kutse ta intanet.

An jiyo sakataren kasa a majalisar dokoki, Stephan Mayer na cewa a cikin watanni masu zuwa za a inganta ayyukan cibiyar kare bayanai ta intanet. Ya ce yanzu haka ma'aikatar cikin gidan na shirin gabatar da sabon daftarin dokar kare bayanai a fannin fasahar sadarwa ta zamani.

A makon da ya gabata dai ne aka tabbatar da labarin cewa masu kutse ta intanet sun saci bayanai na 'yan siyasar Jamus, kana suka yada a shafin Twitter, wanda ya baiwa jama'a da yawa damar ganin wadannan bayanai da aka sata.

Wadanda wannan lamari ya shafa sun hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier.