Jamus za ta fadada aikin hadin kai da kasar Senegal
August 9, 2016Talla
Tarayyar Jamus za ta fadada ayyukan hadin kai da kasar Senegal a fannin koyar da sana'o'in hannu a wani matakin inganta rayuwar 'yan Senegal din da suka koma gida. Ministan ma'aikatar hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus Gerd Müller ya sanar da wannan bayan wata tattaunawa da shugaban Senegal Macky Sall a birnin Dakar, inda ya kara da cewa.
"Dole mu tabbatar da kirkiro guraben aikin yi a kasashen Afirka. Senegal ta zama kasar da 'yan gudun hijira da ke son zuwa Jamus ci-rani, suke yada zango a cikinta. Sakonmu a nan shi ne makomarku na a kasashenku, saboda haka muke zuba jari mai yawa a Senegal da Niger da ma sauran kasashen Afirka."
Yanzu haka dai an ware karin kudi Euro miliyan 10 don habaka ayyukan hadin kai da Senegal.