1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta hana yara kanana amfani da shafukan sada zumunta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 18, 2026

Australia ce kasa ta farko a duniya da ta haramtawa kananan yara 'yan kasa da shekaru 16 shiga shafukan sada zumunta.

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Michael Probst/AP Photo/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya nuna goyon bayansa ga kudurin haramtawa kananan yara amfani da shafukan sada zumunta na zamani a kasar, domin rage mummunan tasirin da shafukan ke yi ga bunkasar rayuwar yaran.

Ko da ya ke shugaban ya ce yana taka-tsan-tsan a kan sanya takunkumin shiga shafukan ga kananan yaran, to amma lallai akwai bukatar bai wa yara kariya daga miyagun dabi'u da suke dauka yayin amfani da su.

Kairn bayani - Taron tsaro a birnin Munich na Jamus

Australia ce kasa ta farko a duniya da ta dauki matakin haramtawa kananan yara 'yan kasa da shekaru 16 shiga shafukan sada zumunta na zamani, inda wasu kasashen Turai da dama su ka fara yunkurin daukar makamancin matakin.