1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta jagoranci taimaka wa kasashen Afirka

Suleiman Babayo
June 12, 2017

A wannan Litinin ne Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da wasu shugabannin kasashen Afirka dangane da shirin rage kaifin talauci da magance matsalolin rikice-rikice da ake samu a nahiyar.

Deutschland G20 Afrika Treffen
Hoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

Ganawar ta zo ne gabanin taron rukunin kasashen G20 da Jamus ke jagoranci wanda zai wakana ranakun a 7 da 8 na watan gobe na Yuli. Daya daga makasudin ganawar dai shi ne na samar da hanyar aiki tare wajen hada karfi da karfe domin ganin nahiyar Afirka ta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki tare da masu zuba jari na kasashen ketare wadanda za su samar da guraben ayyuka.

Wasu daga cikin shugabannin na Afirka sun hada da Shugaba Abdel-Fattah Al-Sisi na Masar da Shugaba Alpha Conde na Guinea wanda yake rike da shugabancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Afirka. Ga ma abin da Angela Merkel ke cewa loacin taron da aka yi a Berlin fadar gwamnatin Jamus.

"Muna sane da cewa babu yadda nahiyar Afirka za ta samu ci gaba da ya dace, sai duk yankunan duniya sun samu ci gaba. Wannan haka yake, nan da shekaru masu zuwa tilas nahiyar Afirka ta bunkasa ta fannoni daban-daban."

Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Angela Merkel ta kara da cewa a shekarun da suka gabata 'yan siyasa sun fi mayar da hankali kan harkoki ci gaba, yayin da lamarin tsaro ya zama a sahun baya, domin haka yanzu za a taimaki nahiyar Afirka ta bangaren tsaro domin yaki da ta'addanci. Ta kuma nuna takaicin yadda rashin fata da makoma ta gari ke tilasta matasa a nahiyar ke gudu daga nahiyar Afirka domin samun rayuwa mai inganci a kasashen Turai.

Martanin kananan kasashen

Tuni mutane kamar Akinwumi Adesina, shugaban bankin raya kasashen Afirka ya nuna gamsuwa.

"Na ji dadi matuka cewa rukunin kasashen G20 na kallon Afirka ta wani fanni, game da ci-gaba wanda haka yake da muhimmanci. Amma yanzu kasashen na kallon Afirka ta bangaren zuba jari, wanda yake da matukar tasiri. Kuma haka na zama martani sakamakon abubuwa da suke faruwa cikin nahiyar Afirkia."

Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Wondimu Hailu

Stefan Liebing ya kasance kusa cikin cibiyar bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Jamus da nahiyar Afirka wanda kuma ya jinjina wa wannan shiri, sannan ya yi kashedin cewa zai fi dacewa a fitar da takamaiman burin da aka sanya a gaba, daga bangaren kasashen na G20 da ma kasar ta Jamus.

Fa'idar Wannan Ganawa

Wani abu mai himmanci da ake dubawa a wannan ganawa shi ne makomar tattalin arzikin Afirka nan da shekaru biyu masu zuwa. Masana daga kungiyar kasashen OECD, mai kula da bunkasar tattalin arziki da na bankin raya kasashen Afirka za su yi muhawara kan makomar nahiyar, cikin masu jawabi har da Shugaba Paul Kagame na kasar Ruwanda.

Ana fata matakan da ake dauka na bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka za su taimaka wajen dakile dubban matasa da a kowace rana suke neman shiga kasashen nahiyar Turai. Jamus wadda ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai ta karbi bakuncin dubban bakin haure a cikin shekarun baya bayan nan. Kuma ita ce ke rike da shugabancin rukunin kasashen na G20 da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki za ta karbi bakuncin taro kasashen a watan gobe na Yuli.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani