SiyasaJamus
Za a rage amfani da takunkumin corona a Jamus
March 18, 2022Talla
Gwamnatin Jamus ta shirya janye manyan dokokin kariya daga corona duk da yawan masu kamuwa da cutar da kasar ta shaida a ranar Alhamis. Scholz ya yi wannan jawabi bayan wani taro na musamman da ya yi da gwamnonin jihohin Jamus 16.
Daga ranar 20 ga watannan na Maris ne dai sanya takunkumin rufe hanci ba zai zama dole ba a shaguna da makarantu. Sai dai kuma za a ci gaba da sanya takunkumin a asibitoci da jiragen kasa da gidajen kula da tsofaffin na kasar ta Jamus.