Jamus za ta kafa rundunar tsaro mai karfi
May 14, 2025
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce sabuwar gwamnatinsa ta hadaka za ta bayar da fifiko kan tsaro da hadin kai da kuma raya ci gaba. Ya ce domin cimma wannan buri akwai bukatar sauyin manufofi ta fuskoki da dama.
Ya baiyana hakan ne yayin jawabinsa na farko a gaban majalisar dokokin tarayya a Berlin. Merz ya ce sabuwar gwamnatin wadda ta kunshi Jam'iyyun CDU da abokan kawancensu na Bavaria CSU da kuma Jam'iyyar SPD suna sane da kalubalen da Jamus ke fuskanta na cikin gida da waje musamman matsalolin kudade. Ya ce Jamus ta na karfi da juriya kuma za ta shawo kan kalubalen.
A waje guda kuma shugaban gwamnatin Friedrich Merz ya bukaci kasashen Turai cewa kada su yarda su rarraba akan Ukraine. Ya ce yana kokarin tabbatar da hadin kai tsakanin Turai da Amurka kan yadda za a kawo karshen yakin.