Cin zarafin mata ya sa kara daukar matakai a Jamus
January 10, 2016
Cin zarafin mata da aka yi a birnin Köln na kasar Jamus a jajiberin sabuwar shekaran nan abin da ake zargin mutane daga Arewacin Afirka musamman Larabawa cikin 'yan gaba-gaba da sa hannu a ciki, wata alama ce da ke nuna cewa dole a kara tsaurara matakan tsaro a lokutan bukukuwean al'adu na Carnival da za a yi a wata mai zuwa a biranen da ke gefen kogin Rhine a cewar jami'an 'yan sanda.
Arnold Plickert shugaban kungiyar 'yan sandan GDP da ke jihar da ke a Yammacin Jamus ya ce ba za a lamunci wani hali ba na rashin da'a daga kowane rukunin al'umma, ganin irin abin da ya faru a wannan lokaci da ake shiga sabuwar shekara wanda koda a jiya Asabar sai da jami'an 'yan sanda suka yi dagaske wajen hana rikidewar zanga-zangar adawa da cin zarafin matan da aka yi a birnin dan kada ta zama tashin hankali.
Wannan lamari dai na ci gaba da jawo suka ga baki daga sassa daban-daban na duniya inda ko a jiya dan takarar shugabancin Amirka Donald Trump wanda akewa kallon me kin jinin baki ya tofa nasa albarkacin bakin.
"Abin da ke faruwa a Jamus abu ne da tunani ba zai dauka ba, wannan kasa ce da ba ta san wannan matsalaba ta cin zarafin mata a baya suna zaune lafiya, amma yanzu da baki sama da miliyan suka shiga ga abin da ke faruwa".