1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ministan Jamus ya bukaci rage tallafin ketare

December 2, 2023

Jamus za ta rage kudaden tallafin kasashen ketare

Hoto: Martin Luy/DW

Ministan kudi na Jamus ya bukaci gwamnatin kasar da ta katse kudaden tallafi da take bawa kasashen duniya a wani mataki na cike gibin kasasfin kudin kasar na shekara ta 2024, kimanin  euro biliyan 17.

Lindner ya ce akwai bukatar Jamus ta gaggauta daukar mataki kan kudaden da ta ke kashewa na kasashen ketare kama daga na sauyin yanayi da raya kasashe masu tasowa da dai sauransu.

Ya kuma kara da cewa, akwai bukatar tunkarar batun marasa aikin yi, wajen sama musu guraben da zasu taimaka wajen ci gaban kasar gadan-gadan.

Kawancen jam'iyyun da ke mulki a Jamus na ci gaba da tattaunawa kan hukuncin kotun kundin tsarin mulkin kasar kan yadda za a shawo batun cike gibin kasafin kudin shekara ta 2024.