1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus za ta rufe sananin sojinta da ke Jamhuriyar Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 6, 2024

Sansanin dai na zama wata tunga ta yakar ayyukan ta'addanci a kasashen yankin Sahel, karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya

Hoto: Carsten Hoffmann/dpa/picture alliance

Gwamnatin Jamus za ta sarayar da sananin sojin samanta da ke birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, bayan da kasashen biyu suka gaza cimma matsaya kan ikon 'yancin aiki da kariya ga sojojin Jamus din.

Karin bayani;Shugabar tawagar dakarun EU ta fice daga Nijar

Ma'aikatar harkokin tsaron Jamus ta ce za ta rufe sansanin a ranar 31 ga watan Agusta mai kamawa, kuma dakarunta za su dawo gida, kamar yadda ta shaidawa majalisar dokokin kasar a birnin Berlin.

karin bayani:Tasirin juyin mulkin Nijar a jaridun Jamus

Sansanin dai na zama wata tunga ta yakar ayyukan ta'addanci a kasashen yankin Sahel, karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya, to amma sun gaza cimma matsaya kan tsarin bayar da horo da kuma makamai.