Dakatar da shirin bututun iskar gas
February 22, 2022A wani mataki na daukar tsauraran matakan ladabtarwa a kan Rasha bisa ci gaba da kokarin mamayar gabashin Ukraine, Jamus ta dauki matakin dakatar da shirin da ta kashe makudan kudi a ciki.
Da yake jawabi ga manema labarau a fadar mulki ta Berlin, shugaban gwamnati Olaf Scholz ya ce wannan mataki nasu na zuwa ne ayayin da kasashen yamma ke tatauna wa a kan jerin takunkuman da za su kakabawa Rasha a kan rikicinta da ta ki janyewa da kasar Ukraine.
Dama dai wannan shirin shigar da makamashin iskar gas daga Rasha zuwa Jamsu na shan suka daga takwarorin Jamus din irinsu Amirka da wasu kasashen Turai, da ke korafin cewar hakan zai sa su kasance masu dogaro da Rasha a wannan bangaren, wanda wasu ma ke ganin musamman a wannan lokacin tana amfani da hakan ne wajen cimma wasu muradunta na siyasa.
Mista Scholz ya ce sun cimma matsayar sake yin nazari a kan wannan shiri wanda dama bai kai ga fara aiki ba.