Jamus za ta shiga cikin aikin lalata makamai masu guba na Siriya
January 9, 2014Talla
Ministan harkokin wajen Tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce kasarsa za ta shiga cikin aikin lalata makamai masu guba a Siriya. Ministan ya fada a birnin Berlin cewa bai kamata Jamus mai kwarewar fasaha a wannan fannin ta ki shiga cikin wannan aiki ba. Saboda haka gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kawar da birbishin sinadaran makaman a barikin rundunar sojin kasar dake garin Munster na jihar Lower Saxony. Ya ce za su yi wannan aiki ne bayan kwararru daga kasar Amirka sun yi daya-daya da makaman masu guba. Kudurin Majalisar Dinkin Duniya dai ya tanadi da a kammala lalata makaman gubar na Siriya kafin tsakiyar wannan shekara da muke ciki.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu