Jamus: Taron kasa da kasa na sake gina Ukraine
September 21, 2023Shugaba Olaf Scholz ya sanar da hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Volodymyr Zelensky a daura da taron kolin na Majisar Dinkin Duniya wanda ke gudana a birnin New York na Amurka.
Manufar taron da za a yi a birnin Belin shi ne taimaka wa Ukraine don ta ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta, da kuma sake gina ababen more rayuwa da yaki ya yi wa illa.
Karin bayani: EU: Sake gina Ukraine da kudaden Rasha
A cikin wani sako da shugaba Zelensky ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce shi da Scholz sun tattauna kan halin da dakarun kasar da ke fagen daga ke ciki da kuma irin bukatocin Kiev don ci gaba da farmakin da ta kaddamar kan dakarun mamaya na Rasha.
Jamus ta sha alwashin ci gaba da tallafa wa Ukraine, baya ga shirinta na ba wa Kiev sabon kunshin tallafi da ya kai miliyan 400 na Euro.
Karin bayani: Ukraine za ta samu karin tallafi daga Jamus