1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaka wa Libiya rungumar tsarin demokaraɗiya

January 8, 2012

Ministan harkokin wajen Jamus ya gana da takwaran aikinsa a birnin Tripoli a inda ya bayyana aniyar ƙasarsa na taimaka wa Libya komawa kan tafarkin demokaraɗiya.

Guido Westerwelle ya gana da firaministan Libya.
Westerwelle ya yi wa firaministan Libiya alkawari.Hoto: dapd

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ya da zango a birnin Tripoli na ƙasar Libya, a ci gaba da rangandin kwanaki huɗu na wasu ƙasashen arewacin Afirka da ya ke yi. Westerwelle ya gana ga shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Abdurrahim al-Kib, da kuma ministan harkokin wajen Libya Ashur bin Kayyal.

A ganawar da suka yi a babban birnin na Libya, ministan harkokin wajen na Jamus ya bayyana wa takwaran aikinsa cewa, ƙasarsa na da niyar taimaka wa Libya fita halin da ta ke ciki domin ta koma kan tafarkin demokaraɗiya. A nasa ɓangaren ministan harkokin wajen Libya Ashur bin Kayyal ya ce gwamnati da ke ci a yanzu ba ta ɗaukan rowar ƙuri'a da Jamus ta yi, lokacin kaɗa ƙuri'ar amincewa da afkwa Gadhafi da yaƙi da wani mahimmaci.

Ita dai Jamus ta bayyana sha'awar zuba jari a fannin gine gine a ƙasar ta Libiya. A ranar asabar ne Westerwele ya fara wannan rangadi a yankin arewacin Afrika da ƙasar Aljeriya. A halin yanzu kuwa, ya zarce a wannan lahadin i zuwa Tunisiya da ke zama zangonsa na ƙarshe.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman