1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta amince ta aika wa Ukraine tankokin yaki

Usman Shehu Usman ZUD
April 26, 2022

A wani mataki da ke nuna sauya alkibla, Jamus ta ce za ta tallafa wa Ukraine da tankokin yaki domin ta kare kanta daga Rasha. A baya Jamus ta rika yin taka-tsan-tsan wurin shiga yakin da ke faruwa a ketare.

Deutschland Ramstein Air Base | PK Verteidigungsminister
Hoto: Boris Roessler/dpa/picture alliance

Ministar tsaron Jamus, Christine Lambrecht, ta ce sun amince su aika wa Ukraine wasu tsaffin tankokin yaki da ka iya harbo jirgin sama. Ministar ta tabbatar da haka a yayin gudanar da wani taron taimaka wa kasar Ukraine wanda kawayenta suka shirya karkashin jagorancin Amirka.

‘‘Irin wadannan tankoki Ukraine ke matukar bukata don kare sararin samaniyarta" in ji ministan tsaron ta Jamus.

 

Yanzu dai kusan a iya cewa kiraye-kirayen Ukraine na neman tallafin makamai ya shiga kunnuwan da suka dace. A wannan taro da ke gudana a Jamus, kasashen da ke halarta na shirin daukar matakin ‘bai- daya’ a game da irin taimakon da za su iya bai wa Ukraine. A wurin taron, Amirka ta lashi takobin tallafa wa Ukraine yin nasara a yakin da take yi da Rasha.

 

Gabanin kiran wannan taron dai, ministocin harkokin waje da na tsaron Amirka sun kai ziyara Kiev, babban birnin Ukraine, inda ministan tsaron Amirka  Lloyd Austin, ya ce ziyararsu a Ukraine ta kara tabbatar masa irin bukatar gaggawa ta kayan yaki da Ukraine ke da ita. Sai dai ministan tsraon Jamus bayan sauraran hakan daga bakin jami’an Amirka ta ce ‘‘idan Ukaraine na bukatar makamai cikin gaggauwa, to muma a nan muna shirye mu ba ta"

 

A wannan Talatar ce dai Amirka ke jagorantar taro na ministocin tsaro daga kasashe 40 na duniya, domin su taimaki Ukraine ta yi nasara a yakin da take yi da kasar Rasha.  Tun a farkon yakin, da aka kwashe kusan watanni biyu ana fafatawa, Ukraine ke ta shelar neman tallafin mamakai daga kawayenta domin yaki da Rasha wace ita ce ta biyu wurin karfin soja a duniya. Sai dai yakin ya zo daidai lokacin da su kan su kawayen Ukraine din irinsu Jamus ke fuskantar kalubale, inda rundunar sojin Jamus ke fadi-tashin ganin ta mallaki sabbin tankokin yaki.