Kotun Jamus ta ce za ta yanke hukunci kan 'dan kasar Gambia
November 27, 2023Kotun Jamus ta ce shirye-hirye sun kammala na yanke hukunci kan tsohon mamba na mayakan Gambia, da ake zargi da keta hakkin 'dan adam da kisan gilla harma da hada baki wajen gudanar da munanan ayyuka.
Karin bayani:Gambiya ta matsa a kan binciken Yahya Jammeh
Mutumin mai shekaru 48 da aka bayyana sunan sa a matsayi Bai L, na da hannu a mutuwar wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya da ke aiki da sojojin Gambia a lokacin da suke gudanar da sintiri.
Karin bayani: Gambiya: Bukatar yanke hukunci ga Jammeh
Babban mai gabatar da karar kotun ta Jamus ya ce Bai L, ya bada gudummuwa wajen murkushe 'yan adawa a lokacin mulkin Yahya Jammeh, ta hanyar jigilar wadanda suke kashe 'yan hamayya a motarsa. A shekara ta 2003, wani lauya ya sha da kyar bayan an bude masa wuta, shekara daya bayan hakan aka kashe wani 'dan jarida. Kazalika a shekara ta 2006 'yan bangar siyasar da aka fi sani da Junglers suka kashe wani babban 'dan adawan Yahya Jammeh.
Karin bayani: Gambiya: Zanga-zangar lumana dan fatan hukunta Yahya Jammeh
An dai cafke wanda ake zargi ne a birnin Hannover, Jamus a watan Maris 2023, tun daga wannan lokaci yake tsare a gidan yari.