Jamus: Zaben 'yan majalisundokoki
March 11, 2016A ranar Lahadi 13 ga watan Maris da muke ciki ne dai za a gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki na jihohin uku a Tarayyar Jamus.
Sai dai batun rikicin 'yan gudun hijira da yadda shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta bude musu kofofin kasar domin shigowa samun mafaka na shirin zama wani bigere na yin duba ga masu kada kuri'a.
Yankin Ellwangen da ke Gabashin jihar Baden-Württembergs ya yi fice sakamakon marabar da al'ummarsa suka yi ga dubban 'yan gudun hijirar. A shekara ta 2015 akalla yankin ya karbi bakuncin 'yan gudun hijira 4.600.
Sai dai a yanzu ana iya cewa yanayin karbar bakin na al'ummar wannan yankin ya samu nakasu a lokaci guda . Shin ko akwai wani mataki da Merkel din za ta dauka kan batun na 'yan gudun hijira? A baya dai Merkel na cewa za su iya:
"Zan iya cewa hakan sabo ne da yadda aka sanmu da yin abin bajinta."
Kimanin mutane sama da miliyan 12 ne dai suka cancanci kada kuri'a a jihohin uku na Baden-Württemberg da Rheinland-Pfalz da kuma Sachsen-Anhalt a zaben na wannan Lahadi.
Koda yake Merkel ta samu goyon bayan wasu jam'iyyun adawa dangane da bude kan iyakokin kasar ga 'yan gudun hijira sai dai ta fuskanci kalubale mai yawa daga jam'iyyarta ta CDU amma tayi nuni da cewar:
"Duk da sukan da ake kan batun 'yan gudun hijirar har yanzu akalla kaso 90 cikin 100 na al'ummar Jamus na ganin ya kamata a tallafa wa 'yan gudun hijirar da ke tserewa tarzoma da cin zarafi,wannan abin na faranta min rai."
A yanzu ana ganin tamkar jam'iyar adawa ta AfD ka iya yin tasiri a Gabashin Jamus, inda a duka jihohin uku ta ke da sama da kaso 10 gabanin zaben na ranar Lahadi. Shugabar jam'iyyar AfD a jihar Baden-Württemberg Frauke Petry na da ra'ayin cewa:
"In aka tsallaka kan iyaka ba bisa ka'ida ba, kana mutumin da ya aikata wannan laifi ya ki bin umurni ya zamo dole a hukunta shi koda kuwa ta hanyar amfani da bindiga ne a matsayin mataki na karshe."
Alamu dai na nuni da cewa jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel din na cigaba da dakushewa a yankin Gabashin kasar, yayin da jam'iyyar AfD ke samun tagomashi.