1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ana ci gaba da juyayi kan harin birnin Hanau

Zulaiha Abubakar GAT
February 20, 2020

A kasar Jamus adadin mutanen da suka mutu a cikin harin da wani dan bindiga ya kai a daren Laraba a wani shagon shan shayi da shisha ya karu zuwa 11, a yayin da wasu da dama suka ji rauni.

Deutschland Hanau | Schießerei & Tote, Angriff auf Shisha-Bars: Sicherkräfte vor Eingang einer der Shisha Bars
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Probst

Masu bincike a Jamus sun tabbatar da samun gawar mutumin da ake zargi da harbe wasu mutane a birnin Hanau na kusa da birnin Frankfurt. A daren Larabar da ya gabata ne wani dan bindiga ya bude wa wasu mutane wuta a wasu tagwayen shagunan shan shayi da zukar shiha a birnin Hanau na Tarayyar Jamus. Nan take mutane tara suka mace yayin da wasu mutum biyar suka samu muggan raunuka. Sai dai binciken da tawagar kwararru a fannin tsaro ta gudanar ya nuna wata mota yayin da take yunkurin, arcewa daga gurin da wannan ta'annanti ya faru gabanin isowar jami'an tsaro.

Rahoton jami'an tsaron ya gano yadda dan bindigar ya yi wani faifan bidiyo inda a ciki yake bayanin cewar hukumar leken asiri mai bangarori dabam-dabam ce ke jagorancin kasar Jamus. Ya kuma yi wasu kalamai masu kaushi kan 'yan gudun hijirar kasashen Larabawa da Turkiyya wadanda ke zaune a Jamus kamar dai yadda kakakin rundunar 'yan sanda Micheal Malkmus ya yi karin bayani:

Hoto: Getty Images/AFP/T. Lohnes

"Masu bincike na aiki, shaidun da muka tattara, wani da abin ya faru a kan idonsa ya bayyana mana cewar an ga wata mota a harabar da harbin ya afku, mai motar wani mutum ne daga Kesselstadt a birnin na Hanau, kuma tuni muka aika da jami'an tsaro na musaman adreshin mai motar da ke unguwar Helmholtstrasse inda muka samu gawarwakin mutane biyu, daya daga cikinsu kuma shi ne ya aikata wannan laifi. Yawan wadanda suka mutu ya kai 11 yanzu domin an sami wata gawa a inda dan bindigar ya fara kai farmaki idan aka hada da mutune takwas da kuma mutane biyu na Helmholtzstrasse".

Isma'il Unaldi wani da al'amrin ya faku a kan idonsa ya yi wa jami'an tsaro karin haske yana mai cewa:

"Na sauko da 'ya'yana biyu kanana, domin gidan iyayena na kusa da mu, sai na ga wasu mutane biyu suna tsaye a "La Votre" shagon shan shisha. Idan zan iya tunawa sun dauki mintuna shida zuwa bakwai domin ta kusa da su na wuce da yarana. Ni da 'ya'yana muna cikin koshin lafiya. Tsakanin gidana da gurin da abin ya faru zai iya kaiwa tsawon mita 100, ina hawa saman bene sai na ji harbin bindiga sau biyar, shida, bakwai iya abin da na ji kenan".
 
Shi ma Ben Mansour wani matashi ne da harbin ya yi sanadiyyar mutuwar kawun abokinsa a shago ya bayyana fargaba:

Hoto: Getty Images/S. Gallup

"An harbe kawun abokinmu a don haka muka zo don jajantawa, ba abin da za mu iya yi a lokacin da abin ke faruwa, duk da cewar ba tsoro ba ne, amma mun fara fargabar shiga ko fitowa daga gidajen sha. 

Da yake jajantawa tare da kwantar da hankalin al'ummar Jihar Hesse inda wanan matsala ta afku, ministan al'amuran cikin gida a jihar Peter Beuth ya danganta harbin bindigar da ayyukan kyamar baki, ya kuma kara da cewar an samu wanda ake zargin da mahaifiyarsa a mace tare da harbin bindiga a jikinsu, ya kuma shaida wa iyalan wadanda suka rasa rayukan nasu cewar masu bincike na aikin gano wasika ko karin bayani a rubuce kamar yadda wasu jaridu suka bayyana.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani