Jamus: Zanga-zangar adawa da dokokin corona
December 28, 2021Talla
Gwamnatin Jamus dai ta sanya sabbin dokokin haduwar mutane tare da haramta zuwa kallon shagulgula gabanin bukukuwan sabuwar shekara. A makwannin baya-bayan nan ne dai zanga-zangar ta yadu zuwa sassa daban-daban a kasar, sai dai kuma a lokuta da dama ta kan rikide zuwa arangama tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma masu zanga-zangar.
Jamus dai na fuskantar barazanar annobar corona a karo na biyar, inda aka samu sabon nau'in cutar mai suna Omicron a jihohin kasar.