1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Zanga-zangar kyamar baki a Köthen

Gazali Abdou Tasawa MNA
September 10, 2018

A kasar Jamus dubunnan jama'a sun gudanar da zanga-zangar kyamar baki a garin Köthen bayan da wani Bajamushe ya rasa ransa cikin fada da wasu 'yan Afganistan.

Deutschland Tödlicher Streit in Köthen - Trauerzug
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Willnow

A kasar Jamus dubunnan jama'a sun gudanar da zanga-zanga kyamar baki a garin Köthen na jihar Saxony Anhalt ta gabashin kasar bayan da wani matashin Bajamushe ya rasa ransa a cikin wani fada da wasu 'yan asalin kasar Afganistan su biyu a daren Asabar washe garin Lahadi. Hukumomin shari'a na yankin dai sun bayyana cewa matashin Bajamushen mai shekaru 22 wanda da ma ke fama da ciwon zuciya ya rasu ne a sakamakon bugon zuciya. 

Tuni dai aka cafke matasan 'yan asalin kasar ta Afganistan tare da tuhumar daya daga cikinsu da laifin bugu da rauni da ya yi dalilin mutuwa. Zanga-zangar wacce ta wakana a bisa kiran jam'iyyar masu kyamar baki ta samu halartar mutane kimanin 2500. 

Sai dai mahukuntan jihar ta Saxony Anhalt na fargabar wannan zanga-zanga ta garin Köthen wacce a wannan karo ta wakana cikin lumana ta rikide a gaba zuwa irin kazamar tarzomar da ta wakana a birnin Chemnitz bayan kisan wani Bajamushe da wani dan asalin kasar Afganistan ya yi.