Jamus zata bi hanyoyin diplomasiya don samun masalaha da Iran
December 12, 2006SGJ Angela Merkel ta sake jaddada kokarin da Jamus ke yi na hana Iran ci-gaba da shirin ta na nukiliya. Lokacin da take magana bayan ganawar ta da FM Isra´ila Ehud Olmert a birnin Berlin Merkel ta ce zata yi amfani da dukkan hanyoyi na diplomasiya don warware rikicin da ake yi da Iran. Shuagbar gwmnatin ta Jamus ta kuma yi Allah wadai da wani babban taro da shugaba Ahmedi Nijad ya kira a Iran don karyata aukuwar kisan kare dangi da aka yiwa yahudawa lokaci yaki duniya na biyu. Shi kuwa a nasa bangaren FM Isra´ila Ehud Olmert ya sake maimata matsayin kasar sa ne cewar ba zata tabbatar ba ko kuma musanta cewa ta na da makamin nukiliya ba. A jiya dai Olmert ya janyo kace na ce a kasarsa bayan ya saka Isra´ila a jerin kasashen duniya masu mallakar makaman nukiliya.