Jamus zata kula da gabar tekun Libanon yadda ya kamata inji Steinmeier
September 8, 2006Talla
Duk da sabbin sharudda da gwamnati a birnin Berlin ta gindaya, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi fatan girke sojojin ruwan Jamus a gabar tekun kasar Libanon. Bayan tattaunawar da yayi da FM Libanon Fuad Siniora a birnin Beirut, Steinmeier ya ce za´a kula da yankunan ruwan kamar yadda aka amince tsakanin MDD da kuma Libanon. Sojojin ruwan na Jamus zasu sa ido don hana yin sumogar makamai zuwa ga mayakan Hisbollah. A dai halin da ake cikin Steinmeier ya isa birnin Kudus inda zai gana da takwararsa ta isra´ila Zipi Livni. A jiya alhamsi Isra´ila ta janye kawanyar da ta yiwa iyakokin sama na Libanon, amma ta na ci-gaba da toshe iyakokin ruwa sabanin sanarwar da ta bayar a ranar laraba. Gwamnati a birnin Kudus ta ce sai dakarun kasa da kasa sun isa yankin ne sannan zata kammala janyewar.