Jamusawa 3 sun mutu a Afghanistan
August 15, 2007Talla
Mutane 3, dukkan su jamusawa su ka rasa rayuka a ƙasar Afghanistan, a cikin wani hari da ya rutsa da tawagar motocin Nato a birnin kabul
Ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir, ya tabbatar da wannan labari.
Ya kuma ƙara da cewar dukan mutane 3 jami´an tsaro ne a opishin jikadancin Jamus da ke birnin Kabul.
Steinmeir ya bukaci gwamnatin ƙasar Afghanistan, ta gaggauta bincike, domin gano mutanen da ke da hannu a cikin wannan ɗayan aiki, ta kuma hukunta su, daidai yadda dokoki su ka tanada.
A yayin da ya jawabi a game da wannan al´amari, ministan cikin gidan Jamus Wolfgang Schäuble, ya ce tunni gwamnatin Taraya ta aika ƙurraru a inda hatsarin ya faru, domin tallafawa jami´an tsaron Afghanistan.