Jamusawa 5 sun rasa rayukan su a Pakistan
October 5, 2010Talla
Aƙalla Jamusawa 5 suka rasa rayukan su, sakamakon wani harin da aka ƙaddamar a yankin arewa maso yamacin Pakistan. Jami'an leƙen asiri na cikin gida a kasar Pakistan, sun ce kimanin mutane 8 ne suka rasu, a wani hari da hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA ta kai a yankin, da jiragen sama masu sarrafa kansu da kansu. 5 daga cikin su Jamusawa ne 'yan asalin kasar Turkiyya. A yayin da aka kai harin, makaman rokoki biyu ne suka lalata wani gida da ke garin Mirali a arewacin Waziristan inda ke da iyaka da ƙasar Pakistan. Yankin na Waziristan ya yi kaurin suna wajen zama maɓoyar 'yan tawayen da ke da alaƙa da ƙungiyoyin Taliban da na Alƙaida.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Umaru Aliyu