1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus:Za a yi shari'ar wadanda suka kitsa juyin mulki a kotu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 1, 2026

A 2025 'yan sanda sun kama mai alaka da su, bayan ikirarin shirin kashe tsoffin shugabanni Angela Merkel da Olaf Scholz.

'Yan sandan Jamus a bakin aiki
'Yan sandan Jamus a bakin aikiHoto: André März/dpa/picture alliance

Mutanen nan uku masu tsatstsauran ra'ayi da gwamnatin Jamus ke zargi da yunkurin juyin mulki da kuma kitsa sace minista, za su gurfana gaban kotun birnin Munich a ranar Laraba.

A 2025 babbar kotun birnin Koblenz ta yanke wa mutanen uku tare da wata mace guda daya hukuncin dauri, tsakanin shekaru takwas da shekaru biyar da kuma watanni tara.

Karin bayani: Jamus ta jaddada yunkurinta na mayar da bakin haure 'yan Siriya a gida

Mutanen sun hada da Achim M mai shekaru 60 da Joachim K mai shekaru 71 da kuma Rainer S mai shekaru 62, wadanda ake zargi da kitsa yin garkuwa da ministan lafiya na lokacin Karl Lauterbach, kan matakansa na lokacin cutar Corona, bisa kudurinsu shirya juyin mulki.

Karin bayani:Rikicin Sudan ya dauki hankulan jaridun Jamus

Ko a cikin watan Nuwamban 2025, 'yan sanda sun kama wani mai alaka da mutanen, wadanda ake kiran kungiyarsu da Reichsbuerger, bayan wasu jawabai da ya wallafa a shafukan sada zumunta da ke ikirarin shirin kashe 'yan siyasa, ciki har da tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da magajinta Olaf Scholz.