Jama'a na yin bankwana da gawar Ayatollah a Iraki
July 8, 2026
Talla
Dandanzo jamaa sun cika tituna da wuraren ibadar 'yan Shi'a da keNajaf, a Iraki, domin rakiyar jana'izar Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei, kafin a bizne shi a mahaifarsa.
A birnin na Najaf,dake a kudancin Iraki, inda gawar Ayatollah ta iso da jirgin sama a ranar Talata da yamma, an yi wa titunan ado da manyan hotunan Ayatollah a wannan rana da aka ayyana a matsayin ranar hutu.
Bayan Najaf, an mayar da akwatin gawar Ali Khamenei zuwa Karbala a arewa, zuwa wuraren ibada na Imam Hussein da ɗan'uwansa Abbas.
Za a bizne gawarsa a gobe Alhamis a Mashhad, mahaifar Ali Khamenei da ke arewa maso gabashin Iran.