Ta'addanciLibiya
Libiya: Jana'izar Seif al-Islam Gaddafi
February 6, 2026
Talla
Birnin na Bani Walid da a nan ne aka yi jana'izar Seif al-Islam Gaddafi da aka bindige har lahira, na da nisan kimanin kilomita 175 da kudancin Tripoli babban birnin kasar ya cika da magoya bayan marigayi Muammar Gaddafi shekaru kusan 15 bayan kifar da gwamnatinsa tare da kashe shi. A yayin guguwar juyin-juya halin kasashen Larabawa da ta gudana a shekara 2011 ne dai, masu zanga-zanga da gudunmawar dakarun rundunar kungiyar Tsaro ta NATO suka halaka Gaddafi.