1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jana´izar Walid Eido

June 14, 2007

A ƙasar Libanon,dubun jama´a su ka halarci jana´izar Walid Eido, ɗan majalisar dokokin nan, mai aƙidar adawa da Syria, wanda wasu yan bindiga su ka harbe jiya, tare da ɗan sa, da kuma ƙarin mutane 8 , a birnin Beyruth.

A kann hanyar makabarta, masu jana´izar sun yi ta rera kalamomi na zargin shugaban ƙasar Libanon,Emil Lahud, da kuma shugaban Syria Bachard Al Assad, da shirya maƙarƙashiyar kashe Walid Eido.

A wurare da dama,na birnin Beyruth,jama´a ta shirya zanga-zanga, tare da yin Allah wadai ga ƙasar Syria.

Ƙasashe daga sassa daban-dabanna dunia na dunia na ci gabada yin Allah da wannan kissa.

Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, ya dangata al´amarin da rashin imani, ya kuma buƙaci Libanon, ta girka komitin bincike, domin gano masu alhakin wanan ɗanyan aiki.

A yayin da ake cikin juyayin mutuwar Walid Eido, dakarun gwamnatin Libanon, da yan takifen Fatah Al Islam, na ci gaba da ɓarin wuta a yankin Nahr Al-Bared.

Daga farkon wannan yaƙi ranar 20 ga watan mayu zuwa yanzu, rundunar gwamnati ta yi asara sojoji 63, a yayin da yan takifen ƙungiyar Fatah Al-Islam, su ka rasa dakaru 50.